Posts

Showing posts from November, 2022

Abin da yasa arewa chin Nigeria suka fi kudu talauchi

'Yan Najeriya ciki har da masana tattalin arziƙi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta fitar, da ke nuna cewa mutum miliyan 133 ko kuma kashi 63 cikin 100 na 'yan ƙasar ne ke fama da talauci. Rahoton ya ce kashi 65 cikin 100 na matalautan Najeriya wato mutum miliyan 86, suna zaune ne a arewa. Rahoton ya bayyana Ondo a matsayin jihar da ta fi ƙarancin matalauta da kashi 27 cikin 100, Yayin da Sakkwato ta fi yawan matalauta inda kashi 91 na 'yan jihar ke fama da talauci. Masana dai na cewa akwai tazara mai karfi tsakanin masu arziki da talaka, duk da cewa kasar mai arziki ce talakawanta sun fi yawa. Sai dai ko mene ne dalilin da ya sa talauci ke karuwa a arewa? Talauci a arewcin Najeriya Farfesa Kabiru Isa Dandago, masanin tattalin arziƙi a Jami’ar Bayero da ke Kano ya shaidawa shas cewa Najeriya na cikin wani yanayi saboda kaso mai yawa na tattalin arzikin kasar na hannun mutane tsiraru. Ya ce kididdiga da aka fitar a kan hanya take,...